ABNA24 : Jaridar ‘The News Times’ ta kasar ta bayyana cewa gwamnatin ta dauki wannan matakin ne bayan taron majalisar ministocin kasar a jiya Laraba.
Labarin ya kara da cewa dokar hana fitar za ta ci gaba da aiki har zuwa kwanaki 9 inda banda fita don ayyuka na lalura wadanda suka hada da sayan abinci da magunguna.
Har’ila yau dokar ta shafi manya-manya da kananan makarantu a wadannan yankuna in banda wadanda suke shirin daukar jarrabawar karshe.
Banda wannan gwamnatin ta takaita fita zirga-zirga a wasu yankunan daga karfe 6 na yamma har zuwa 4 na safe na tsawon wadannan kwanaki.
Ya zuwa yanzu dai mutane 10,761 suka kamu da cutar ta Covid 19 tun bayan bullarta shekaru biyu da suka gabata, a yayinda mutane 160 daga cikinsu suka rasa rayukansu.
342/